A 21 GA WATAN NAN NAHCON ZA TA YI TARO DA HUKUMAR HAJJI TA SAUDIYYA KAN AIKIN HAJJIN 2023

A ranar 21 ga watan nan na Disamba hukumar alhazan Najeriya NAHCON za ta yi taro da hukumar hajji da umrah ta Saudiyya kan shirin aikin hajjin 2023.

Taron dai zai gudana ne ta na’urar yanar gizo inda za a fara daga karfe 10.30 na safe agogon Saudiyya.

Jami’ar labarun HANCON Fatima Sanda a wata sanarwa ta baiyana cewa hukumomin Saudiyya sun turo takardar tabbatar da gudanar da taron ta ma’aikatar wajen Najeriya.

A na sa ran a taron za a zanta kan yanda a ke sa ran farashin kujerar hajji za ta kasance musamman kuma farashin hidima a Muna, Muzdalifah da Arfa.

Hakanan za a tattauna kan bukatar dawo da kudin hidimar da jami’an hidimar alhazai a Saudiyya na MU’ASSASA ba su gudanar yanda ya dace ba.

Taron zai zama share fagen shirin rantaba hannun yarjejeniyar gudanar da aikin hajjin tsakanin Najeriya da Saudiyya da hakan ne ka’ida a duk shekarar da za a gudanar da aikin na ibada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *