ZABAR ATIKU NE KADAI ZAI FIDDA AREWA DA NAJERIYA DAGA HALIN KAKANI-KAYI-ATTAHIRU BAFARAWA

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce hanya da ya ke ganin za ta fidda ‘yan arewa da Najeriya dga kakani-kayi ita ce zabar dan takarar PDP Atiku Abubakar a 2023.

Bafarawa na magana ne a lokacin da ya ke baiyana ra’ayin kan huldar da ya ce ya yi da dan takarar PDP Atiku da na APC Bola Ahmed Tinubu.

Bafarawa wanda shi kan sa ya fito neman takarar shugabancin kasa a baya, ya ce lokaci ya yi da jama’a za su farka su zabi wanda ya kware da jagoranci ba la’akari da jam’iyya ko bukatun kashin kai ba.

Duk da Bafarawa jigo ne yanzu a PDP, ya ce ya na da hasashen cewa hatta ‘yan APC za su marawa Atiku baya don ceto Najeriya daga kalubalen tsaro dama barazanar ‘yan aware.

A kalaman na Bafarawa tamkar APC a kaikace ta sarayar da matsayin shugabancin kasa ga PDP ne lokacin da ta zabi Tinubu a matsayin dan takarar ta ga babban zaben.

A na sa bangare jigon APC Farouk Adamu Aliyu bah aka ya ke gani ba, don a ra’ayin sa mika ragama ga Tinubu ne zai hade kan Najeriya da magance barazana.

Har yanzu dai batun arewa da kudu a jagaorancin kasa bai kare ba hakanan gwagwarmayar tazarce ma na daga al’adar ‘yan siyasar Najeriya.

A nan sai a ce ba a gane maci tuwo sai miya ta kare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *