Kafafen yada labaru musamman na yanar gizo sun cika da labarin yanda jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya goce daga kan titin sa.
Jirgin dai ya taso daga Kaduna ne inda daf da tsayawa a tasha a Abuja kan sa ya goce daidai inda zai dau saitin kwana.
Duk baynaan da a ka samu sun nuna duk fasinjojin sun samu ficewa daga jirgin ba tare da samun raunuka ba kuma ba wanda hakan ya sa a ka kai asibiti.
Lamarin ba zai tsiritar da jama’a sosai ba don ya auku ne a yankin cikin gari kuma ba wata barazana wasu za su kai hari kan jirgin inda a ce lamarin a daji ya auku.
Har yanzu dai ba a samu ainihin dalilin da ya haddasa gocewar jirgin ba.