A na kara nuna fatar babban bankin Najeriya CBN zai tsawaita lokacin daina aiki da tsoffin kudi don dimbin ‘yan kasa su samu canja kudin su.
Kiraye-kirayen daga kusan duk masu fada a ji na kasar ya sa a na ganin bankin dai gabanin 31 ga watan zai tsawaita wa’adin.
Mutane sun yi ta garzayawa bankuna don yin canji amma dogon layi da damuwar ba sabbin kudin ya haddasa rudanin gaske da kuma nuna bacin rai a fili.
Bannkuna a asabar din nan sun bude don cigaba da aikin yi wa mutane canjin ko dai akalla a ce samun damar zuba kudin a asusu.
Daina karbar tsoffin kudin da wasu ‘yan kasuwa su ka yi musamman a yankunan karkara ya jawo karin zullumi a tsakanin jama’a da ke kara karfafa barazanar samun babban kalubale.