RUNDUNAR TSARON FARAR HULA SIBIL DIFENS TA MIKA SAURAN GAWAR JAMI’AN TA 4 GA IYALIN SU DON BISO

Rundunar tsaron farar hula ta Najeriya SIBIL DIFENS ta mika sauran gawar jami’an ta 4 ga iyalin su don yi mu su biso.

Jami’an 4 na daga cikin 7 da ‘yan bindigar daji su ka yi wa kisan gilla a yankin karamar hukuamr Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Sauran jami’an dai an yi mu su jana’iza gabanin guda hudun.

Da ya ke ganin karshe don girmamawa ga jami’an da su ka mutu a bakin aiki, shugaban rundunar na kasa Audi Abubakar ya ce rundunar ta girgiza da rasa jami’an.

Audi ya ce ba wani mai rai da ba zai dandani dacin mutruwa ba, don haka jami’an Allah ya hukunta ta haka za su bar duniya kuma kowa na jiran lokacin sa.

Babban kwamandan ya kara da cewa hukuma za ta duba diyyar da za ta mikawa iyalin marigayan, duk da ba diyyar da za ta maye gurbin rai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *