INA SON SHUGABA BUHARI YA BA NI NNAMDI KANU NA AJIYE SHI A AWKA DON ZAMAN LAFIYA-SOLUDO

Gwamnan jihar Anambra Charles Soludo ya bukaci shugaba Buhari ya mika ma sa ragamar kula da shugaban ‘yan awaren Biyafara na IPOB Nnamdi Kanu don zaman lafiya a yankin kudu maso gabar mai rinjayen ‘yan kabilar Igbo.

Soludo na magana ne a taron kaddamar da kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar sa ta APGA Peter Umeadi a Awka babban birnin jihar ta Anambra.

Soludo ya dau alwashin har dai a ka bas hi Kanu zai iya kawo shi a duk lokacin da a ke bukatar sa kuma zai taimaka mu su ne wajen samar da zaman lafiya.

Gwamnan na Anambra wanda ya taba caccakar dan takarar jam’iyyar Leba Peter Obi da nuna bai kama hanyar lashe zabe ba, zai iya amfani da wadannan maganganu wajen samun goyon bayan jama’ar Igbo da wasun su ke kaunar aiyukan Kanu na raba kasa.

A wani lokaci da a baya dattawan Igbo su ka ziyarci shugaba Buhari don bukatar a sake kanu, ya ce zai duba duk da an san ba ya sa baki a harkar kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *