MUN SAMU MAN FETUR A JIHAR NASARAWA-NNPC

Kamfanin man feture na Najeriya NNPC ya baiyana cewa aikin binciken sa ya sa ya gano man fetur a jihar Nasarawa arewa ta tsakiyar Najeriya.

Hakan ya fito ne daga bakin shugaban kamfanin Mele Kyari Kolo a lokacin da ya ke karbar bakuncin gwamnan jihar Abdullahi Sule da ya kai ma sa ziyara.

Kyari Kolo ya ce an gano man ne a yankin Keana ta yamma kuma za a aiyana cewa jihar Nasarawa na da man a watan Maris.

Wannan na cikin cigaba da aikin binciken man fetur ne a cikin doron kasar Najeriya wato a yankunan arewacin kasar.

In za a tuna kamfanin ya tabbatar da hako man fetur a rijiyoyin KOLMANI da ke tsakanin jihar Gombe da Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *