DAN TAKARAR PDP ATIKU ABUBAKAR YA DAWO DAGA TAFIYAR DA YAYI

Dan takarar babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP Atiku Abubakar ya dawo daga tafiyar da ta kai shi London daga Dubai.

An yayata cewa tafiyar ta Atiku na da nasaba da ganin likita ne kamar yanda manyan Najeriya kan garzaya London in sun ji ba su ganewa jikin su ba.

Kakakin dan takarar Paul Ibe ya musanta batun rashin lafiya inda ya ce Atiku ya shiga London ne bisa gaiyatar jami’an gwamnatin kasar.

A lokacin ziyarar Atiku ya gana da minister mai kula da lamuran cigaban Afurka Andrew Mitchel da kuma babban jagoran majami’ar Canterbury Reverend Justin Welby.

Gwamnan Akwa Inom Udom Emmanuel da gwamnan jihar Sokoto Waziri Tambuwal na tawagar dan takarar a matsayin masu rakiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *