Hukumar tsaron farin kaya DSS ta cafke tsohon mai ba wa shugaba Jonathan shawara ta hanyar farafaganda Doyin Okupe inda ta mika shi hannun hukumar yaki da cin hanci EFCC.
DSS ta kama Okupe a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos a lokacin da ya ke shirin tafiya London.
Duk da dalilan tafiyar ta sa kan duba likta ne, amma an samu labarin dan takarar jam’iyyar sa ta Leba Peter Obi zai gabatar da jawabi a Chattam House da ke London din.
Daga bisani EFCC ta ce an kama Okupe bisa wani umurnin yin hakan tun 2016 kuma an kama shi daidai lokacin da hukumar ke shirin janye bukatar.
Okupe ya tabbatar da cafke shi da a ka yi, ya na mai cewa an sake shi kuma jami’an EFCC a Lagos da Abuja sun ba shi hakuri kan hakan.