Wasu kungiyoyin fararen hula sun gudanar da zanga-zanga a bakin babban bankin Najeriya CBN su na bukatar a kwabe gwamnan bankin Godwin Emefiele.
Wannan ya zama wuni na biyu na gudanar da irin wannan zangar ta barranta ga Emefiele da bukatar shugaba Buhari ya kwabe shi daga mukamin.
Kungiyoyin da su ka hada da na matasa na zargin Emefiele da daukar matakan da ke durkusar da tattalin arzikin Najeriya da kuma shiga lamuran badakala.
Emefiele wanda ya shiga jam’iyyar APC har ya so neman tikitin takara don gadon shugaba Buhari, ya fara aiki ne tun mulkin tsohon shugaba Jonathan inda bayan karewar wa’adin sa a zamanin shugaba mai ci Muhammadu Buhari, ya sake samun damar sabon wa’adi.
Canja fasalin kudi da takaita daukar kudi a na’ura na daga cikin abubuwan da gwamna nya kawo a baya-bayan nan da sam bas u burge akasarin ‘yan Najeriya ba.