Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya shigo Najeriya a sace amma kuma nan da ‘yan kwanaki kalilan zai sake ficewa ketare.
A binciken da jaridar yanar gizo ta PREMIUM TIMES ta wallafa, ya nuna Emefiele ya shigo Najeriya a asoirce ranar laraba inda zai zauna na ‘yan kwanaki kalilan kafin ya sake juyawa.
Jaridar ta ce ta samu tabbacin hakan daga majiyoyi a babban bankin da kuma fadar Aso Rock.
Duk da haka wata majiya a cewar jaridar ta ce dama shugaba Buhari ya amince Emefiele ya yi hutun mako biyu kuma hutun ya kare don haka ya dawo bakin aiki.
Hakika bayanan sun fahimtar da jama’a cewa Emefiele na buya ne don gudun kar hukumar tsaron farin kaya DSS ta cafke shi.
DSS na binciken Emefiele kan badakala da kuma tura makudan kudi ga kungiyoyin ta’addanci ta hanyar amfani da wasu masu mu’amala da kudi.
Za a jira a ga yanda gwamnan bankin da ke cikin rikici zai baiyana a gaban jama’a ne ko kuwa a’a.