Hukumar kula da ‘yan sanda ta Najeriya ta baiyana cewa ita ke da hakkin daukar kananan jami’an ‘yan sanda kama daga kurata zuwa mataimakan sufuritenda.
Wannan ba wata sabuwar takaddama ba ce tsakanin hukumar da ofishin babban sufeton ‘yan sanda wanda a zamanin tsohon babban sufeto Muhammad Adamu har sai da a ka gurfana gaban kotu.
Jami’an labarum hukumar Ikwchuckwu Ani ya baiyana matsayra hukumar bayan wani mataki da ma’aikatan hukumar su ka dauka na zanga-zangar cikin gida ta hana manyan jami’ai fita har sai sun baiyana daukar mataki kan zargin sarayar da hurumin hukumar ga babban sufeton.
Ani ya ce ai hukuncin kotun daukaka kara ya tabbarwa hukumar hurumin daukar kananan jami’an; don haka hukumar ta dauki wannan a matsayin hakkin ta bisa tanadin tsarin mulki.
Hakanan ma’aikatan sun tado da maganar jinikirin rashin karin girma da tafiya horon kwarewa na bara daga hukumar.