‘Yar siyasa Binta Abubakar daga jihar Filato ta ce ita ce mace ta farko Bahaushiya da ta taba tsayawa neman tikitin takarar majalisar wakilai daga karamar hukumar Jos ta kudu a jihar ta Filato.
A zantawa ta musamman kan lamuran siyasar mata, Binta Abubakar ta ce an samu maza Hausawa da su ka jarraba takarar a yankin amma a mata ita ce ta fito don neman kujerar da zummar ba da gudunmawar ta wajen raya arziki da zaman lafiyar jihar.
Duk da ba ta samu tikitin ba, Binta ta ce zuciyar ta ba ta karye ba kuma in Allah ya yarda za ta cigaba da gwada tsayawa har ta cimma gaci.
Binta Abubakar ta ce yanzu mata sun fara sauya tsari inda su kan marawa mata ‘yan uwan su baya a takarar siyasa.
Hakanan ta ce an samu nasarar mata masu mutunci na shiga siyasa da hakan ya rage ganin mata masu harkar siyasa a matsayin ‘yan bariki.