MANYAN ‘YAN SIYASA DA IYAYEN GIDA NA MARA BAYA A FILI GA ‘YAN TAKARAR DA SU KE SO

Gabanin babban zaben Najeriya a watan gobe, manyan ‘yan siyasa da iyayen gida na fitowa karara su mara baya ga wanda su ke ganin ya dace da ra’ayin su.
Wannan ma ba sabon abu ba ne a irin wannan lokaci don mara bayan kan nuna inda kowa ya fuskanta a zaben.
Dukkan ‘yan takarar na fitattun jam’iyyu na samun irin wannan mara baya amma hakan ba ya na nuna abun da talakawa za su zaba ba ne.
Kamar mara baya da Obadanjo ya yi wa Peter Obi maimakon tsohon mataimakin sa Atiku Abubakar ko Bola Tinubu, ya jawo martani daga sauran jam’iyyun da ke cewa ba wani tasiri da hakan zai yi.
A wani yanayin ma mai nuna siyasar bangaranci, dattijon Neja Delta Edwin Clerk ya mara baya shi ma ga Peter Obi inda a ka ruwaito shi ya na cewa kungiyar ‘yan jihohin kudu maso kudu ta mika muradu ga Obin.
In za a tuna yayin da wasu ‘yan siyasa mabiya addinin kirista na arewa su ka kaucewa tafiyar Tinubu an samu bambancin ra’ayi inda cikin su tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya mara baya ga Atiku shi kuma tsohon sakataren gwamnati Babachir David Lawal ya mara baya ga Obi.
Talakawa masu kada kuri’a ke da ta cewa a zaben inda maganar su kan baiyana ne a akwatin zabe fiye da kafafen labaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *