Rundunar tsaron farin kaya ta DSS ta cafke wanda a ke tuhuma da tada bom a jihar Kogi mintuna kadan gabanin isowar shugaba Buhari da ya je ziyarar aiki don bude aiyuka a jihar.
Mutumin mai suna Abdulmumin Otaru ya tada bom din a yankin karamar hukumar Adavi gabanin shugaba Buhari ya zo inda a sanadiyyar hakan mutum 4 su ka rasa ran su.
Kakakin rundunar DSS Peter Afunanya ya baiyana hakan a sanarwa inda kuma a ka kama Otaru da abokin aikin sa mai suna Sa’idu Sulaiman.
Tashin bom din bai hana shugaba Buhari zuwa yankin ba inda ya bude wata cibiyar lafiya bisa gaiyatar gwamnan jihar Yahaya Bello.
Afunanya ya ce an gano cewa Otaru dan kungiyar ISWAP ne ta Afurka ta yamma da ke mubaya’a da kungiyar DAESH ta duniya.