ZAN TSIGE KOWANE BASARAKE KO MAI MUKAMI MATUKAR YA CIGABA DA YI MIN HA’INCI-GWAMNA INUWA YAHAYA

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce zai tsige duk wani basarake ko mai mukamin gwamnati matukar ya cigaba da aiyukan manufurci ko ha’inci gabanin babban zaben 2023.

An ji gwamna Yahaya ya na furta kalaman ne a wani faifan sauti da a ka dauka a ziyarar sa a karamar hukuamr Akko.

Gwamnan wanda da alamu ya na gargadin wasu ne da ke neman yi ma sa angulu da kan zabo a babban zaben tazarce na 2023, ya fito karara ya ce zai saka kafar wanda daya da duk mai bin bayan fage ya na kulle-kulle.

Inuwa Yahaya wanda ya fara neman kujerar gwamna a jihar ta arewa maso gabar tun 2011 ya samu nasarar lashe zabe a 2019 inda bayan wani lokaci ya samu sabani da tsohon gwamnan jihar Muhammadu Danjuma Goje.

Gwamnan ya kafa sharadin duk mai kaunar sa ya zauna da shi wanda kuma ya ke son bin Goje shi ma ya tafi don ya ja layi kan dambarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *