An dakatar da kasar Burkina Faso daga kungiyar tarayyar Afrika

Kungiyar tarayyar Afrika, ta dakatar da kasar Burkina Faso daga zamowa daya daga cikin ‘ya’yanta, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi ma shugaba Koch Marc Chiristian Kabore a ranar 24 ga Janairun wannan shekara.

Kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar mai mambobi 15, ya bayyana a shafinsa na Twitter a yau Litinin cewa, Majalisar ta yanke shawarar ta dakatar da kasar Burkina Faso daga ci gaba da  dukkan ayyukan kungiyar har sai an maido da tsarin mulkin kasar yadda ya kamata. “An sanar a cikin wani sakon twitter da kwamitin tsaro da zaman lafiya, mai kula da rikice-rikice da batutuwan tsaro na kungiyar ta Afrika (AU).

Tuni dai Moussa Faki Mahamat, shugaban kungiyar ta Tarayyar Afirka ya yi Allah wadai da juyin mulkin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *