Yan Sanda Sun Hallaka Wasu Yan bindiga A Katsina

Rundunar Yan sandan jihar katsina ta samu nasarar hallaka wasu yan bindiga da sukayi yunkurin kawo hari a kauyen badole na karamar hukumar kurfi dake jihar katsina
Yan sandan sun kuma yi nasarar kwato dabbobi da dama da yan bindiga suka sato
Kamar yadda kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina S.P. Gambo Isah ya bayyana rundunar kalkashin jagorancin jami’in yan sandan karamar hukumar Kurfi sunyi nasarar dakile mummunar aniyar yan bindigar lokacin da suka tunkaro kauyen suka kora wasu tarin dabbobi
Ya bayyana cewa rundunar hadin gwiwar wadda ta kunshi yan sandan da yan sintirin sun samu nasarar tare hanyar da yan bindigar suka biyo a kauyen yan runfar koza dake karamar hukumar
“Rundunar sun tunkari yan bindigar inda suka samu nasarar hallaka da dama daga cikin su bayan sunyi musayar wuta tare da kwato dabbobi da dama wadanda yan bindigar suka sato”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *