GWAMNA AMINU BELLO MASARI YA BADA UMARNIN BUDE KASUWAR SHANU.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya amince da gaggauta bude gidajen mai da kasuwannin shanu da aka rufe a baya saboda satar shanu da kuma ‘yan fashi da makami a jihar.

Masari ya kuma umurci Masarautun biyu na jihar da su gargadi Hakimai na yankunan da abin ya shafa da su yi taka-tsan-tsan tare da tabbatar da cewa ba za a amince da duk wani aiki na hadin gwiwa na Sarakunan Fawa da sauran su ba.

A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Mustapha Muhammad Inuwa ya sanyawa hannu ta yi gargadin cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sake kafa dokar rufe inda aka ga sake bullar duk wani shakku.

An rufe gidajen mai da kasuwannin da abin ya shafa, a wani bangare na dokar kalubalantar tsaro da gwamnati ta bayar na takaita samar da mai ga ‘yan fashi da kuma hada-hadar cinikin dabbobin da aka sace a jihar.

Sanarwar ta samu sa hannun Abdullahi Aliyu Yar’adua Daraktan Yada Labarai na Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *