Gwamna Masari ya tabbatar da cewa gwamnati na kokarin bullo da sabbin dabaru na murkushe ‘yan fashi da makami.

Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce gwamnatinsa na hada kai da masu ruwa da tsaki domin samar da sabbin dabaru da za su kawo karshen kalubalen tsaro da wasu sassan jihar ke fuskanta a halin yanzu.

Gwamna Masari ya tabbatar da hakan a yayin taron tunawa da Sojojin Najeriya na shekarar 2022 da runduna ta 17 ta Sojojin Najeriya ta Katsina ta shirya.

Gwamnan ya ce ranar tunawa da sojojin ta kasance wata hanya ce ga gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki don samar da karin hanyoyin taimakawa iyalan jarumai da suka sadaukar da rayuwarsu domin kare martabar Najeriya da Afirka da ma duniya baki daya.

Alhaji Aminu Bello Masari ya yaba da irin gudunmawar da Jaruman da suka fadi a kan fafutukar da suke yi na ganin Najeriya ta kasance kasa daya.

Yayin da yake yaba da jajircewar Sojoji wajen yaki da ayyukan ‘yan bindiga a jihar, Gwamnan ya bada tabbacin gwamnatocin sa na ci gaba da bada goyon baya ga fafutukar da suke yi domin samun nasarar da ake bukata.

Bikin na bana ya yi nuni da shimfida furen ado a Dogon Yaro Tumb, fareti masu launi da kuma shiru na mintuna uku da harbin bindiga guda uku don karrama jaruman da ke fadowa.

Bikin na shekara ya samu halartar shugaban majalisar dokokin jihar Katsina da shugabannin hukumomin tsaro na jihar da wakilan sarakunan Katsina da na Daura da sauran manyan baki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *