Za’a Buɗe Gidan Rediyo Mai Gajeren Zango A Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Da Ke Katsina

Shirye-shirye sun yi nisa domin buɗe Gidan Rediyo Mai Gajeren Zango(F.M) A Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.

Dalilin buɗe gidan rediyon shi ne domin samun damar amsar saƙonni daga al’ummar Jihar Katsina, don samun cigaba mai ɗorawa.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Sanusi Mamman ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a kan nasarorin da Jami’ar ta samu a ƙarƙashin shugabancin sa.

Kamar yadda Farfesa Sanusi Mamman ya tabbatar, a halin yanzu jami’ar tana jiran amincewar Shugaban kasa ne kawai, wanda shi ne ke da hurumin bada lasisin buɗe gidan rediyo a Ƙasar nan.

Farfesa Sanusi Mamman ya yi magana mai tsawo akan ɗumbin nasarori da jami’ar ta samu da suka hada da gina gidaje 80 da gwamnatin jihar ta yi, domin amfanin malaman jami’ar, da kuma wani tsarin bashi mai saukin biya da jami’ar ke baiwa malaman ta, domin inganta rayuwar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *