Iyalan Yan Sanda Da Suka Rasa Rayukan Su A Katsina Sun Karɓi Kuɗi Sama Da Naira Miliyan 50
Kwamishinan Yan Sanda na Jihar Katsina CP.Shehu Umar Nadada, ya gabatar da chakin kuɗi sama da naira miliyan 50 ga iyalan Jami’an Rundunar da suka rasa rayukan su a cikin aiki.
CP. Shehu Umar Nadada ya gabatar da chakin kuɗin ne ga iyalan da suka amfana a Babban Ɗakin Taro na Hedikwatar Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina, kuma Accuracy News 24/7 ta shaida.
Iyalai 15 ne na jami’an Yan Sanda da suka rasa rayukan su suka amfana da wannan tagomashi, domin rage raɗaɗin rashin yan uwansu da suka yi.
Gabatar da kuɗin ga iyalan ya biyo bayan amincewar Babban Sufeto Janar na Yan Sandan Najeriya, a wani ɓangare na shirin Inshora ta Hukumar Yan Sandan Najeriya.
A sa’ilinda yake miƙa sakon ƙara yin ta’aziya na Babban Sufeto Janar na Yan Sandan Najeriya ga iyalan mamatan, Kwamishina Shehu Umar Nadada ya yi kira garesu akan su yi kyakkyawan amfani da kuɗaɗen da aka basu domin inganta rayuwarsu.
Ya nanata ƙudirin Babban Sufeto Janar na Yan Sandan Najeriya na cigaba da yin bakin ƙoƙarin shi ta fuskar inganta rayuwar Yan Sanda da kyautata jin daɗin su.
Wasu daga cikin iyalan da suka amfana, sun godewa Babban Sufeto Janar da Kwamishinan Yan Sandan akan inganta rayuwar su ta fuskar bayar da kuɗaɗen.