Ƙalubalantar2023: Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Kai Gabanta Na Ƙalubalantar Takarar TinubuƘalubalantar

2023: Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Kai Gabanta Na Ƙalubalantar Takarar Tinubu

Wata Babbar Kotun Tarayya Da Ke Zama a Abuja ta yi watsi da wata ƙara da aka shigar a gaban ta, ana ƙalubalantar sahihancin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC Sanata Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2023.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Kwamitin Yaƙin neman zaɓe na Ɗan Takarar ya fitar Bayo Onanuga.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, ko a makwannin da suka gabata, sai da kotun ta yi watsi da wasu ƙararraki da aka shigar gabanta inda ake ƙalubalantar sahihancin takarar Tinubu ɗin.

Daga cikin ƙararrakin akwai wadda jam’iyyar AC ta shigar da shi akan rashin canchantar yin takara da kuma bijire wa umarnin kotu.

Kamar yadda yake a cikin ƙarar mai lamba, CS/854/2022, Mai Shari’a Faɗima Aminu Muritala ta bayyana cewa wanda ya shigar da ƙarar baya da cikakkin hujjojin ƙalubalantar ɗan takarar.

Wannan dai shi ne karo na huɗu da aka watsar da ƙara da ta danganci irin wannan lamari na ƙalubalantar sahihancin Ɗan Takarar.

Watsar da ƙarar ta wannan karon ya biyo bayan roƙon da lauyan wanda ake ƙara Julius Ishola Esq, ya yi wa kotun akan cewa ƙarar bata da makama ko tushe, kuma ɓata lokacin Shari’a ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *