FaɗuwaBan Taɓa Faɗuwa Ko Wane Irin Zaɓe Ba – Tinubu Ga BabachirFaɗuwa

Ban Taɓa Faɗuwa Ko Wane Irin Zaɓe Ba – Tinubu Ga Babachir

Dan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa bai taɓa faɗuwa zaɓe ba tun da ya shiga harkokin siyasa.

Sai dai, Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal, ya furta cewa Tinubu ba zai ci zaɓe ba a 2023, sabili da ya ɗauki Musulmi a matsayin abokin takarar shi.

Da yake maida martani ta bakin Daraktan Yaɗa Labarai na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen, Bayo Onanuga, Tinubu ya bayyana kalamun Tsohon Sakataren Gwamnatin a matsayin waɗanda basu da makama ko tushe.

Ya ce ” kalamun abin dariya ne domin Asiwaju bai taɓa faɗuwa zaɓe ba a duk lokacinda ya shiga cikin takardar kaɗa ƙuri’a.

” Da Jihohi 22 da APC ke jagoranta, ga kuma goyon bayan Shugaban Ƙasa, Asiwaju shi ne zai lashe zaɓe mai zuwa”.

” Yana da kyau Babachir ya ji da matsalar da ke cikin gidan siyasar shi, maimakon mayar da hankali akan batun da bai dame shi ba akan sakamakon zaɓe”.

” Wannan mutumen da ke neman kawo mana banbancin addini shi da yan gidan siyasar shi, ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Hong ta Ƙaramar Hukumar Adamawa, ya kasa cima Buhari zaɓe a yankin shi a zaɓen shekarar 2019, duk da cewa akwai kiristoci da dama a yankin nashi, saboda haka baya da wani tasiri a siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *