Rashin abinci mai gina jiki: sama da yara milyan daya suka kamu da cutar Tamowa a gabashin Najeriya

Hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya, ta bayyana cewa, kimanin yara sama da milyan daya ne suka kamu da cutar Tamowa a gabashin Najeriya.

Hukumar ta ce, “kimanin yara milyan daya da dubu saba’in da hudu ne suka kamu dacutar Tamowa a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.” Hukumar ta kara da cewa, “ kananan hukumomin Machina da Yusufari da Nguru da Bade da Bursari da Gaidam a jihar Yobe sun fada hadarin rashin abinci mai gida jiki daga wanatan Satumba zuwa na Disamban shekarar da ta gabata.

A cikin wata takarda da hukumar ta fitar, ta ce, bisa nazarin da hukumar ta yi daga wataan Satumba zuwa Augustan shakarar da ta wuce ta 2021, Jimillar yara milyan 1.74 dake tsakanin watannin shidda zuwa hamsin da tara, na fama da matsalar Tamowa a jihar ta Yobe da Borno da Adamwa, daga cikin adadin dubu dari da sha hudu( 614,000)suna fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki, yayin da milyan daya da dubu dari da ashirin da tara (1,129,000) ke fama da matsanancin rashin abinci mai inganci.

A Rahoton da jami’in sadarwa mai kula da babban ofishin hukumar na Maiduguri, Folashade Adebayo, ya fitar, ya nuna cewa, dukkanin kananan hukumomi 11 da suka rage a jihar Yobe, suna cikin mawuyacin hali muddin ba an tashi tsaye ba ko kuma aka amince da matakin tantance matsalar karancin abinci mai gina jiki a tsakanin yara.

Binciken da aka gudanar a jihohi uku na Borno da Yobe da Adamawa, ya nuna “Matsalolin rashin abinci mai gina jiki ya yi yawa a yankuna da dama tsakanin watan Satumba da Disamba 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *