Jami’anJami’an Soji Sun Kakkabe Maboyar Boko Haram 5 Tare Da Hallaka Wasu Daga Cikin Yan Ta’addarJami’an

Jami’an Soji Sun Kakkabe Maboyar Boko Haram 5 Tare Da Hallaka Wasu Daga Cikin Yan Ta’addar

Daga Zagazola Makama

Jami’an Sojin Najeriya sun bayyana cewa sun Kakkabe maboyar yan Boko Haram guda biyar tare da hallaka wasu mutane da ake zargin Yan Kungiyar ta Boko Haram ne a yankin Mafa da ke Jihar Borno.

Rohotanni sun bayyana cewa, Jami’an Soji da ke aiki a Bataliya ta 24 hadin guiwa da takwarorin su na Operation Hadin Kai da Jami’an Sa Kai, sun tsunduma a aikin laluben Yan Boko Haram da maboyar su a yankin Bulakulari da Gwarigwazo da Limanti da Laskori da gami da Kauyen Gaza.

Wata Majiyar Sirri ta sanar da Zagazola Makama Makama cewa, Jami’an sun yi kwallin kura ne da Yan Boko Haram din a lokacinda suke suntiri a yankin Tafkin Chadi, kuma sun hallaka biyar daga cikin su.

Majiyar ta ce Jami’an a Karkashin Laftanar Kanal. Obiyanyo, sun hallaka yan ta’addar da ke buya a yankin suna hallaka sojoji da yan kasa fararen hula da basu ji basu gani ba a yankin Ngwom Mafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *