Wasu Al’ummomi A Karamar Hukumar Batagarawa Sun Koka Akan Rashin Kayayyakin More Rayuwa A Yankin Su
Al’ummomin Kauyen Makurdi-Kuidawa da ke a Karamar Hukumar Batagarawa ta Jihar Katsina, sun yi roko ga Gwamnati akan ta sama masu Kayayyakin more rayuwa a yankin nasu.
Al’ummomin dai sun maganta ne ta bakin Kungiyar cigaban Makudi Kwanar Dutse, inda suka koka akan rashin wadataccen ruwan sha da na amfanin yau da kullum.
Shugaban Kungiyar, Salisu Umar, ya bayyana cewa, tuni al’ummar yankin ke bukatar samun kayayyakin more rayuwa, sai dai hakan bai samu ba.
A cewar shi, al’ummar yankunan na da bukatar hanya da zata hada su da inda zasu samu ruwan sha da na amfanin yau da kullum.
Sauran wadanda suka maganta kamar Malam Abubakar Salisu da Alhaji Ibrahim da Nasiru Aliyu, sun bukaci sama masu da wutar lantarki a yankin, domin cigaban Tattalin Arzikin su, baya ga sama masu da Makarantar Firamare domin llimin ya’yan su.
Al’ummomin sun lashi takobin goyon bayan shirye-shirye da tsare-tsaren Gwamnatin Masari, sai suka yi roko akan bukatar kawo masu dauki, domin su amfana da romon demokradiyya.