Babu Mutum Daya Tak Da Zai Ce Tinubu Ya Taba Cin Amanar Shi Akan Alkawarin Da Suka Yi – Cewar Honorabul Fatuhu Muhammad
Dan Majalissar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Daura/Sandamu/Mai’adua Honorabul Fatuhu Muhammad, ya bayyana Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC Sanata Ahmed Bola Tinubu a matsayin mutum mai amana da baya saba alkawari a duk lokacinda aka yi amana da shi.
Honorabul Fatuhu Muhammad na magana ne a lokacin wani taro da ya shirya hadin guiwa da wata Kungiyar Goyon Bayan Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar APC Sanata Ahmed Bola Tinubu mai suna 100% Focus Movement.
A cewar shi, lokaci ya yi da mutanen Jihar Katsina zasu saka wa Tinubu alkairan da ya yi masu, domin kuwa ya taimaka wurin daga darajar mutane da dama yan Jihar Katsina da suka samu cigaban rayuwa.
” Da dama daga cikin wadanda Tinubu ya taimaka suna tare da Jama’a, kuma suna bakin kokarin su wurin ganin sun taimaki mabukata, a sabili da haka zaben Tinubu Alkairi ne ga mutanen Jihar Katsina.
Ya ja hankalin yan Jihar Katsina akan su kauracewa yan siyasa masu neman a fasa kowa ya rasa, su zabi Bola Ahmed Tinubu domin yana da karfin daukar jama’a ya kai su gachi.
Daga nan sai ya lashi takobin cewa zai yi bakin kokarin shi wurin yanin Tinubu ya lashe dukannin kuri’un yankinda ya fito