Likitan bugi ya yiwa ‘yan mata 4 fyade a jihar Neja

Likitan bugi ya yiwa ‘yan mata 4 fyade a jihar Neja

Rundunar ‘yan sanda a jihar Neja ta kama wani matashi dan shekara 24 mai suna Clement Joseph bisa zarginsa da nuna kansa a matsayin likita tare da yiwa ‘yan mata hudu fyade. A cewar rundunar ‘yan sandan jihar, Joseph ba shi da takardar shaidar da za ta nuna cewa ya cancanci zama likita. An tattaro cewa wanda ake zargin wanda ke gudanar da wani asibiti ba bisa ka’ida ba a yankin Koropka da ke jihar, baya ga yi wa ‘yan matan hudu fyade, ya yi wa daya daga cikinsu ciki, sannan ya zubar da cikin. Kakakin rundunar ‘yan sandan, Abiodun Wasiu, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wanda ake zargin ya kuma amsa laifin damfarar N200,000 daga hannun wani jama’a da ba a san ko su wanene ba, a karkashin wata sana’ar bogi ta yanar gizo mai suna Zuga coins international business. Mujallar Gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *