AN YI WA MARIGAYI BALARABE MUSA ADDU’AR CIKA SHEKARU 2 DA RASUWA

AN YI WA MARIGAYI BALARABE MUSA ADDU’AR CIKA SHEKARU 2 DA RASUWA

Daga Imrana Abdullahi

Dokta Ibrahim Balarabe Musa, madakin kaya Walin Guga kuma Dulban Kilba, babban dan marigayin ne,jim kadan bayan kammala addu’ar cewa ya yi da jama’a Za Su Yi Kamarsa marigayi Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, Da An Zauna Lafiya, domin mafi yawan lokuta ma hatta kudin da ya dace su a matsayin yayan marigayin ya ba su sai kawai ya dauka ya ba wa jama’a kawai ba ruwansu.

Dokta Ibrahim Madakin Kaya, ya ci gaba da fadakar da jama’a cewa “Marigayi baya son zalunci ko wani abu na Haramun kuma kowa nasa ne”.

“Ya na son jama’a fiye da yayansa, koda safe idan an kawo masa abinci kai da kake Bako ne  zaka fara ci kafin shi ya ci abincin saboda son jama’a kawai, a mafi yawan lokuta zaka ga a koda yaushe gidan nan a bude yake kuma mutane Talakawa na zuwa ko ya na nan ko baya nan kullum jama’a zuwa kawai suke yi”.

Madakin Kaya ya kara da cewa ” hakika mun tabbatar da cewa marigayi Mahaifin mu bai ciyar da mu da abin Haramun ba kuma ya yi mana horo da koyi mu guje mata, domin mutum ne mai taka tsan tsan da gudun abin duniya kamar yadda duniya ta shaida hakan”.

Sai Dokta Ibrahim Abdulkadir Balarabe Musa ya fadakar da yan siyasa masu son rungumar jam’iyyar PRP da cewa ita fa, jam’iyyar ce mai tsarki, mai tsarki ce domin ita PRP abu ne da yake a cikin zuciya kawai don haka kowa ya tsarkake zuciyarsa domin a samu ci gaba, saboda duk wanda zai rungumi jam’iyyar PRP ya Sani fa ba maganar kudi bace, hakuri, jajircewa da rikon gaskiya da Amana ce kawai”.

“Masu kokarin siyasa idan ba su da zuciyar marigayi Balarabe Musa ba to lamarin ba zai yuwuwa, kowa ya san hakan”.

“Duk wadanda za su yi PRP to lallai su Sani ba domin kudi bane zuciya ce kawai”.

Alkali Suhaibu Abubakar

An haife ni a 1946, ya ce Malam Balarabe bashi da Kwadayi ko kadan, wannan jama’a ya dace su san hakan.

“Tun a NEPU Malam Abdulkadir Balarabe Musa sun hadu da Malam Aminu Kano, amma mu ko a can asali, mu ba mu isa jefa kuri’a ba amma mu ne yan Gabagadi”.

“A kan PRP marigayi Malam Abdulkadir Balarabe Musa ya sayar da Gonarsa naira miliyan Arba’in domin kawai lauyoyi suyi aiki a ceto PRP, ko fura ba a sha a cikin gidansa ba”.

Dokta Halliru Umar shugaban riko ne na jam’iyyar PRP reshen Jihar Kaduna, ya bayyana rashin Uba kuma shugaban jam’iyyar na kasa marigayi Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa a wani babban rashin da duniya ta yi. Sai ya bayar da tabbacin cewa, amma duk da haka ba za su yi kasa a Gwiwa ba wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar har sai hakarsu ta cimma ruwa na dalilin da yasa aka kafa PRP tun asali. 

Alh Ibrahim Yusuf, hakika na zauna da marigayi Balarabe Musa, kuma ina ganin kila har abada ba zan samu irin sa ba

Da yake tofa albarkacin bakinsa wani mutumin da ya yi zama da marigayin tun da dadewa sama da shekaru 40 tun ya na dan karami a kauyen da Gonar marigayin take Alh Ibrahim Yusuf, hakika na zauna da marigayi Balarabe Musa, kuma ina ganin kila har abada ba zan samu irin sa ba.Domin shi mutum ne mai kokarin ganin rayuwar talaka ta inganta a koda yaushe.

“Har akwai wani lokaci can wasu shekaru baya da rashin lafiya ya rika samun Jarirai da kananan yara a kauyukanmu, wanda daga baya sai aka gano cewa matsala ce ta ruwan da ake sha a wurin, marigayi Balarabe Musa ne ya rika sayo ruwan Gora irin na zamani da kamfanoni ke yi ya na kawo mana muna shayar da yaran mu domin gujewa kamuwa da wannan cutar, ga dai abubuwan alkairi nan da damar gaske da marigayin ya rika yi mana har tsawon rayuwarsa”.

Mista Mark, kuwa cewa ya yi a matsayinsa na cikakken memba na PRP da ya dade tare da marigayin ya fahimci cewa, “Idan da za a samu yan siyasa su yi hali irin nasa da komai ya ta fi da kyau kamar yadda kowa ke fatan a samu”.

Dimbin jama’a da suka hada da malamai makaranta alkur’ani mai girma suka taru a gidan marigayin inda aka yi addu’o’in nemawa mamacin gafara, kuma daga nan sai aka dunguma aka ta fi wajen kabarin marigayin nan ma aka yi masa addu’a.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *