‘Yansanda sun ceto mutane 27 daga hannun ‘Yan ta’adda a jihar Zamfara.

‘Yansanda sun ceto mutane 27 daga hannun ‘Yan ta’adda a jihar Zamfara.

A ci gaba da kokarin dawo da zaman lafiya da inganta harkar tsaro a jihar Zamfara, rundunar ‘Yansandan jihar karkashin jagorancin Kwamishinan’Yansandan jihar Kolo Yusuf ta kara samun wata gagarumar nasarar ceto wasu mutane 27 na kauyukan Akawa da Gwashi da Tungar Rogo da kuma Anka daga gungun ‘Yan ta’adda a sansaninsu dake dazukan Gando/Bagega da kuma Sunke a Kananan hukumomin Bukkuyum da Anka.
Jami’in hulda da Jama’a na Rundunar’Yansandan jihar SP Mohammed Shehu ya bayyana cewar cimma wannan nasarar ya faru ne sanadiyyar rahoton da rundunar ta samu cewar wata tawagar ‘Yanta’adda sun kai hari ga kauyuka, inda suka yi awon gaba da mutane da dama, suka kuma tasa keyarsu zuwa dazuka Gando da Bagega da Sunke tsawon makonni biyu.
A cewar Jami’in, samun rahoton ke da wuya, sai Kwamishinan ‘Yansandan jihar ya hada wata karkarfar tawagar jami’an rundunar hadi da manyan Jami’an ‘Yansandan yankunan Kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da kuma jajirtattun ‘yan sa kai da kuma shugabannin Kananan hukumomin biyu domin ceto mutanen, aka kuma cimma nasarar hakan.
A halin da ake ciki yanzu, goma sha bakwai daga cikinsu na a Hedikwatar’Yansandan jihar domin jin ba’asin yadda abin ya faru, yayin da sauran guda goma na asibiti domin duba lafiyarsu.
Daga bisani Rundunar ‘Yansandan ta mika dukkan mutanen ga Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, wanda a madadin Gwamnan jihar zai mika su ga iyalensu.
Ya bayyana cewar Kwamishinan’Yansandan jihar ya yaba da kokarin jami’an rundunar da kuma jajircewa da Gwamnan jihar yake yi ta fuskar goyon bayan da yake ba bangaren tsaro, ya kuma ba ‘Yansandan jihar da sauran hukumomin tsaro kwarin gwuiwar ci gaba da kokarin da suke yi ta fuskar magance matsalar tsaro a jihar.
Kwamishinan ‘Yansandan har ila yau ya taya mutanen da aka ceto murna tare da bayar da tabbacin cewar rundunarshi ba zata yi kasa a gwuiwa ba wajen jajircewa ga aikin ceto jihar daga matsalar tsaro da take fuslanta.

SP Mohammed Shehu Anipr,
Police Public Relations officer, by
For : Commissioner of Police,
Zamfara State Command
Gusau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *