Matsalar fari ta tilastawa makiyaya ‘yan kabilar Maasai saida shanunsu

Matsalar fari ta tilastawa makiyaya ‘yan kabilar Maasai saida shanunsu.

Matsalar fari ta sanya Shanu sun zamo raunana tare da tagayyara sanadiyyar karancin abinci, mummunan halin da makiyaya’yan kabilar Maasai a kasar Kenya suka shiga a kokarin ganin shanunsu sun rayu cikin yanayin farin da aka shiga a kasar.
Ba karamin muhimmanci kiwon dabbobi ke dashi ba ga rayuwa da kuma al’adar kabilar Maasai, ba kawai ga babbar hanyar abinci da samun kudaden gudanar da harkokin yau da kullum ba, wani abu ne na daukaka matsayi, domin idan akwai Shanun tare da su abin alfahari ne da suke kira Kraals.
Kenya da makwabtanta Habasha da Somalia na fuskantar matsanancin fari a cikin shekaru 40, domin basu sami ruwan sama ba har tsawon shekara 4, wanda hakan ya haddasa mace-macen dabbobi da konewar shuke-shuke a wasu yankunan kasashen, lamarin da ya haddasa matsananciyar yunwa.
Wani mai safarar dabbobi Joshua Kedoya ya bayyana cewar farashin dabbobi a kasuwanni ya fadi warwas domin ramewar da suka yi saboda rashin abincin da zasu ci su yi daraja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *