Wanda ya sace ni, Naira 2,000 ya bani kudin mota..

Wanda ya sace ni, Naira 2,000 ya bani kudin mota..

Wata Hajiya Fatima Ibrahim da aka sace ta bayyanawa wata babbar Kotu a Zaria a matsayin shedar cewar wadanda suka sace ta har Naira 2,000 suka bata ta yi kudin mota bayan sun karbi Naira Miliyan 6 a matsayin kudin fansa.


‘Yansanda dai sun caji Dalhatu Shehu da Lawal Aliyu Bullet da Nuhu Sama’ila da kuma Nura Usman da zargin hada bakin aikata manyan laifukka da fashi da makami da mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba da kuma yin garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa.


Laifukkan da ‘Yansandan suka ce sun sabawa hurumin sashe na 59 karamin sashe na 1 da sashe na 246 a da b a cikin baka na kudin shari’a na Penal Code da kuma sashe na 6 na b a cikin baka na dokar rike bindiga ta musamman.


Hakiya Fatima na bada sheda ce a lokacin da aka ci gaba da zaman sauraren karar da aka shigar a kan satarta da aka yi ga reshen Babbar Kotu ta daya ta Kaduna dake Dogarawa Zaria.


Ta bayyana cewar ranar 2 ga watan Janairu da dare, ta ji wata hayaniya a gidan da take, amma a lokacin da ta tashi ta kunna hasken lantarki, sai kawai taga wadannan mutanen su hudu rike da bindiga da kuma adduna.


Ta bayyana cewar sun bukaci ta nuna inda mai gidanta yake, inda tace masu ya yi tafiya, sai suka sace ni zuwa dajin Galadimawa a Karamar hukumar Giwa bayan sun kwashe kudade da suturun yara da kuma sauran kayayyaki a gidan.


A cewarta, sun kira Mai Gidanta inda suka yi yarjejeniyar za a basu Naira Miliyan 6 ta hanyar biyansu kashi biyu.
A gabana aka basu kudin kuma wanda ake tuhuma na hudu wato Usman ya bani Naira 2, 000 daga cikin kudin in yi kudin mota.


Ta kuma bayyanawa Kotun cewar wadanda ake tuhumar sune suka nuna mata inda zata hau mota zuwa gida tare da bata tabbacin cewar babu abin da zai sameta.


Lauyan dake kare wadanda ake kara ya tambayi Hajiya Fatima da ta fadi sunan wanda aka aiko da kudin ga wadanda ake tuhuma, tace bata san sunanshi ba amma ta san yana aiki tare da Mai Gidanta.


Bayan Kotun ta sallami Hajiya Fatima, sai Kotun wadda Mai Shari’a Kabir Dabo ya jagoranci zamanta ya dage shari’ar sai ranar 15 ga watan Nuwamba domin ci gaba da sauraron karar.


Tun farko sai da Magatakardan Kotun ya karanto wata wasika daga Hukumar kula da gyaran hali ta Nijeriya dake Zaria cewar wanda aka kara na biyu Aliyu Bullet ya mutu, inda takardar ke dauke da shedar hakan daga Babban Asibitin Gambo Sawaba dake Zaria.


Don haka nema Alkalin Kotun Mai Shari’a Dabo ya soke sunan mamacin daga wadanda ake kara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *