Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Dala Miliyan 100 Wajen Ciyar Da Dalibai.

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Dala Miliyan 100 Wajen Ciyar Da Dalibai.

Gwamnatin Tarayya tace ta kashe kimanin Dala Miliyan 100 wajen ciyar da dalibai Miliyan 10 a karkashin Shirin Ciyar da Daliban Makarantun Firamare a fadin kasar nan.
Ministan Kwadago da samar da guraben aikin yi Sanata Chris Ngige ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin Jakadar Amurka a Nijeriya Mary Leomard a wata ziyarar ban girma da ta kai mashi ranar Juma’a a Abuja.
Ministan ya bayyana cewar wannan wani bangare ne na kawar da matsalar bautar da kananan yara a kasar nan.
Ngige yace gwamnatin kasar nan ta kirkiro da shirin ciyar da daliban makarantun firamare a karkashin shirin inganta tsaro domin kawar da kananan yara daga fadawa aikin bautar da kai.
Yace gwamnatin tarayya ta kuma bullo da shirin bayar da kariya domin yaki da fatara, wanda a cewarsa itacee babbar silar da ta bada babbar gudunmuwa ga yawaitar bautar da kananan yara a kasar nan.
Daga nan sai ya yabawa gwamnatin Amurka game da tallafin da ta ba Sashen Kwadago a Afirka ta Yamma.
Ministan ya kara da cewar iyalai masu karamin karfi na tura kananan yaransu su yi aiki a gonakin Cocoa da filayen hakar ma’adinai da tallace-tallace a kan tituna.
Ministan har ila yau ya bayyana cewar bada shawara kadai ba zata kawo raguwar matsalar ba, domin mawuyacin abu ne a jawo hankalin wanda ke cikin akubar yunwa.
Don haka ne ya jaddada bukatarshi a babban taron da aka yi na AGOA cewar ya zama wajibi ga Amurka ta taimaki Nijeriya ta fuskar yaki da bautar da kananan yara ta bangaren bunkasa hazakar aiki da samar da kayan aikin.
Tun farko sai da Jakadiyar Amurka a Nijeriya Leomard ta nuna damuwa a kan ganin yadda kananan yara a Nijeriya suke fadawa matsananciyar bauta a filayen fasa duwatsu da sauran makamantansu.
Ta bada tabbacin cewar kasarta zata ci gaba da yin aiki da gwamnatin kasar nan wajen magance matsalar, sannan ta yi kira ga sauran jihohi bakwai da har yanzu basu fara aiki da dokar ‘Yancin Kananan yara ba da su aiwatar da ita ba tare da bata wani lokaci ba.
Tace gwamnatin Amurka ta nuna jin dadinta ganin yadda aka bullo da sabbin shirye-shiryen dake samar da jari ga masu karamin karfi a yankunan da lamarin bautar da kananan yara ya yi kamari a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *