Mazauna Jihar Kano Sun Yabawa Gwamnatin Tarayya A Kokarinta Na Bunkasa Ilimi.

Mazauna Jihar Kano Sun Yabawa Gwamnatin Tarayya A Kokarinta Na Bunkasa Ilimi.

Mazauna Jihar Kano sun jinjinawa Gwamnatin Tarayya a kokarin da take yi na bunkasa matsayin ilimin manyan makarantu kamar yadda shirin kasafin kudin da ta gabatar a ranar Juma’a.
Wani ma’akacin gwamnati a jihar Muhammed Abubakar yace yunkurin hakan shine ya nuna zimmar gwamnati ta bangaren Ilimi a kasar nan.
Yace mutane ne zargin gwamnati a kan yajin aikin Kungiyar ASUU, amma ya kamata mu yi la’akarin cewar ita kanta gwamnati ta nuna bacin ranta a cikin jawabin da Shugaban Kasa ya yi wajen ganatar da Kasafin Kudin.
Wani dan jihar ma Mustapha Wada yace Kasafin Kudin ya nuna zimmar gwamnati ta fuskar magance matsalar yajin aikin Kungiyar ASUU.
Ya bayyana cewar ga duk gwamnatin da ta shirya kasafin Naira Biliyan 470 domin biyan albashi da magance sauran matsalolin dake barazana ga harkar Ilimi, alama ce dake nuna jajircewa.
Ya yi fatar ganin an kirkiro da sabbin kafofin samar da karin kudade domin daukar dawainiyar ilimin manyan makarantu a kasar.
Shima wani Tireda Mista Mathew Okafor dake Kasuwar Sabon Gari ya yabawa kokarin gwamnati wajen inganta harkar Ilimin manyan makarantu a kasar nan.
Yace gwamnati ta yi gaskiya cewar daukar dawainiyar ilimin manyan makarantu a kasashe daban-daban ya zamo na hada hannu ne ba a bar gwamnati ita kadai ba.
Okafor ya kuma roki Kungiyar ASUU da ta yi la’akarin halin da kasar take ciki, ga matsalar talauci ga kuma yajin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *