Rundunar Tsaron Farin Kaya Ta Cafke Mutate 8 Dauke Da Man Fetur Da Ake Zargin Gurbatacce Ne.
Rundunar Tsaron Farin Kaya ta cafke wasu mutane takwas da ake zargin suna hada-hadar Gurbataccen man fetur a jihar Anambra.
Kwamandan Rundunar Mista Isdore Chikere ya bayyana cewar an cafke wadanda ake zargin ne a ranakun 5 da 6 ga watan Okutoba a garin Awka.
Kwamandan yace wadanda aka cafken sun hada da Ahmed Luka da John Sani da Mohammed Sani da kuma Ali Ahmed Jafar dukkansu daga jihar Nassarawa.
Ya bayyana cewar an cafke su ne da misalin karfe 9:30 na dare a wata babbar mota dauke da gurbataccen man fetur..
Kwamandan ya kara da cewar an cafke sauran mutanen hudu yayin da suke sauke gurbataccen man a wani gidan mai a Umuokpu dake Awka.
A cewarsa, sun hada da Christian Atser da James Tersoo daga jihar Binuwai, sai Jerry Agar daga jihar Nassarawa da kuma Silas Motoko daga jihar Kwara.
Mista Chikere yace Tankokin daukar Mai guda biyu, daya nada lambar Nassarawa KRV 825 XB daya kuma lambar Bauchi BAU 595 XR, kowace na dauke litar mai 40,000 an kuma kama gurbataccen man da suke dauke da shi.
Kwamandan Rundunar ya danganta nasarar hakan a kan ingancin dubarun aikin da Rundunar ta yi amfani da su, ya kuma gargadi dilolin dake shigo da irin wannan man da su fice daga jihar.
Ya jinjinawa Kwamanda Janar din Rundunar Dokta Ahmed Audi da kuma Gwamnan jihar Chukwuma Soludo a kan goyon bayan da suke ba rundunar.
Daga nan sai ya bada tabbacin cewar rundunar zata ci gaba da gudanar da aikinta na kare muhimman kadarorin gwamnati a fadin jihar, sannan ya bayyana cewar za a gabatar da kamammun a gaban hukumar da ta dace.