Gwamnan Atku Bagudu ya amince da a biya Naira Miliyan 151 ga daliban jihar dake karatu a Indiya.
Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya amince da a biya dalibai ‘yan asalin jihar su 116 dake karatu a Indiya Naira Miliyan 151.
Wata sanarwa da Babar Sakatare a Ma’aikatar kula da Ilimi mai zurfi ta jihar Hajiya Halima Dikko ta sanyawa hannu a ranar Juma’a, ta bayyana cewar Kudaden sun kumshi na makaranta da na masauki da Inshorar lafiya da kuma na kashewa a zangon karatu na 2022/2023.
Sauran dalibai dake son yin karatun aikin Likita wadanda ake cikin nema masu guraben karatun a Jami’oin dake kasashen Misira da Rasha dake karkashin amincewar Gwamnan, da zarar Hukumar bada tallafin karo karatu ta kammala cika ka’idodin Jami’oin, za a waiwaye su.
Sanarwar ta bayyana cewar Ma’aikatar ta yi amfani da wannan dama wajen sanar da dukkan dalibai’yan asalin jihar cewar gwamnati na nan na kokarin magance yajin aikin da Kungiyar ASUU ke cikin gudanarwa.
Ta kara da cewar, a halin da ake ciki, tattaunawa ta yi nisa tsakanin gwamnatin jihar da mahukuntan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta jihar domin dawowa aiki a ci gaba da daukar darussan zangon karatu 2023.
Don hakan ne ma Ma’aikatar ta nuna jin dadin kokarin da Gwamnan ke yi na ci gaban matasan jihar ta fannin samun nagartaccen ilimi da kuma bunkasa rayuwarsu.