Shugaba Muhammadu Buhari yace hakurin da ‘yan Nijeriya suka yi ba zai fadi kasa banza ba.

Shugaba Muhammadu Buhari yace hakurin da ‘yan Nijeriya suka yi ba zai fadi kasa banza ba.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewar hakuri da juriyar da ‘yan kasar nan suka yi ba zai tafi hakanan ba, domin salon shugabancisa na ci gaba da sake fasali da karfafa ayyukan hukumomin tsaro domin magance matsalolin tsaro.
Shugaban ya bada tabbacin ne yayin da yake yi wa ‘yan Nijeriya jawabi ranar Asabar domin murnar cikar kasar nan shekaru 62 da samun ‘yancin kai.
Ya bayyana cewar yayin da Gwamnati ke kokarin magance matsalolin tsaro dake fuskantar kasar nan a farkon wannan gwamnati, sai kuma wasu sabbin launikan matsalolin tsaro suka bayyana, Mussamman satar mutane da gallazawa da kuma kashe rayukan da basu ji ba basu gani ba, wanda a halin yanzu ake kan magance su.
Buhari bayyana cewar shi kanshi yana jin radadin da ‘yan kasar nan ke ji, ya kara bada tabbacin cewar hakuri da juriyar da ‘yan kasar nan ke nunawa ba zasu tafi hakanan ba.
Ya jaddada cewar tun lokacin da wannan gwamnatin ta hau mulki, yake samar da Kudaden da hukumomin tsaro ke bukata, inda a cewarsa an kuma kara inganta hakan a kashi na biyu na shugabancinsa a 2019 domin basu damar magance matsalar tsaro kuma za a ci gaba da yin hakan har sai kwalliya ta biya kudin sabulu
Buhari ya yi la’akarin cewar, domin magance matsalolin tsaro, gwamnatin tarayya ta gudanar da aiki cikin dubaru wajen rage ta’addanci a Shiyyar Arewa maso Gabashin kasar nan da yankin Neja Delta da nuna bambancin yare da Addini da kuma sauran matsalolin dake barazana ga kasar nan.
Ya hakkake cewar bullo da yin amfani da Asusun bai daya tare da rage kashe kudade ga harkar shugabanci sun taimaka wajen kawar da matsin tattalin arzikin kasar nan.
Ya yi nuni ga ‘yan kasar nan cewar shugabansa ya kawar da tababa ga masu son zuba jari a bangaren man Fetur da Gas sanadiyyar samar da dokar kafa masana’antar albarkatun mai ta 2021
Wannan ci gaban, a cewarsa ya kirkiro da da wata dama ga masu son zuba jari ‘yan kasar waje kari ga inganta baje komi a faifai na tafiyar da harkokin bangaren.
Game da samar da abinci, Shugaban ya bayyana cewar shugabancinsa ya ba bangaren noma muhimmanci ta hanyar wasu shirye-shirye a Hukumar bunkasa kanana da matsakaitan sana’oi inda hakan ya jaza samar da miliyoyin guraben aikin yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *