Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya dawo daga tattakin da ya yi Kasar Turai.
Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya dawo gida Nijeriya bayan kwashe makonni biyun da ya yi a Kasar Turai.
Mai Shugaban shawara a harkokin yada Labarai Mista Simon Imobo Tswam ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya rabawa manema Labarai ranar Juma’a a Abuja.
Yace Ayu, wanda ya bar kasar nan ranar 14 ga watan Satumba ya sauka Abuja ta Filin jiragen saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe da misalin karfe 7:00 na dare.
Idan za a iya tunawa, Iyorchia Ayu ya mika ragamar tafiyar da Jam’iyyar ga Naibinsa dake kula da Shiyyar Arewa Ambasada Iliya Damagun sannan ya sanar da hakan ga Hukumar INEC.