Wata Kotu ta tsare wani da ake zargin ya kashe Jami’an ‘Yansanda guda biyu.

Wata Kotu ta tsare wani da ake zargin ya kashe Jami’an ‘Yansanda guda biyu.

A ranar Alhamis ce wata Kotun Majistare dake zamanta a Makurdi ta bada umurnin a tsare wani Msughter Orfega dan kimanin shekaru 34 a Cibiyar Gyaran Hali a kan zarginshi da kashe wasu Jami’an’Yansanda biyu.
Ana tuhumar Orfega dake zaune a garin Daudu a Karamar hukumar Guma jihar Binuwai da hada baki a aikata laifi da fashi da makami da kisan kai da kuma halayyar ta’addanci.
Alkalin Majistaren Mista Vincent Kor ba saurari rokon Orfega ba a kan rashin hurumi, don haka ya dage sauraron karar har sai ranar 1 ga watan Nuwamba.
Tun farko sai da Dan sanda mai gabatar da kara ya shedawa Kotun cewar Ofishin ‘Yansandan ciki na garin Makurdi ne ya karbi karar a wata wasika daga Hedikwatar ‘Yansanda na Yanki dake garin Daudu a ranar 28 ga watan Yuni 2022.
Ato ya bayyana cewar wani Sufeton ‘Yansanda Luka John dake rundunar ‘Yansanda ta jihar Binuwai dake aiki a bangaren Yelwata a garin Guma ne ya kai rahoton matsalar a Ofishin ‘Yansanda dake Guma a ranar 23 ga watan Yunin 2022.
John ya yi zargin cewar a ranar 23 ga watan Yuni 2022 suna gudanar da aikin binciken ababen hawa a Ikyogen a Yelwata sai wasu gungun batagari dauke da makamai suka kai masu farmaki.
Ya bayyana cewar nan take batagarin suka harbe Sufeton’Yansanda Christopher Eigege da Sajent Sunday Idoko suka kuma tafi da bindigoginsu.
Ato yace Orfega na daya daga cikin gungun batagarin wanda a halin yanzu yake tsare yayin da sauran da aka aikata laifin tare da su suka gudu.
Laifin a cewar Ato ya sabawa tanadin sashe na 6(b)(1)(2)(a)(b) na dokar fashi da makami da kuma dokar mallakar bindiga ta Kundin Dokar Penal Code ta jihar Binuwai ta 2004 da kuma sashe na 4(2) na dokar data haramta satar mutane da garkuwa da mutane da Kungiyoyin asiri da makamanran irin laifukkan na jihar Binuwai na 2017.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *