Sabon Kwamishinan ‘Yansandan jihar Kwara ya sha alwashin gudanar da aikinshi a tsanake.
Sabon Kwamishinan’Yansandan jihar Kwara Mista Paul Odama ya sha alwashin gudanar da aikinshi a tsanake ga lamurran da suka shafi Siyasa a jihar a lokacin da gudanar da yakin neman zabe.
Odama ya tabbatarwa dukkan Jam’iyyun Siyasa tare da ‘yan takararsu cewar zai kamanta adalci madamar sun mutunta doka.
Sabon Kwamishinan ‘Yansandan, wanda ya nuna haka a lokacin da yake yi wa manema Labarai bayani a Hedikwatar ‘Yansanda dake garin Ilorin ranar Alhamis, ya sha alwashin dorewa tare kara bunkasa zaman lafiya da harkar tsaro da ke akwai a jihar.
Ya yi amfani da wannan dama wajen gargadin masu karya doka da masu aikata manyan laifukka a jihar da su canza dabi’a su zamo masu bin doka da oda ko kuma su kwashe yanasu yanasu su bar jihar.
Odama yace a shirye Rundunar ‘Yansandan jihar take ta yi aiki da bangarorin tsaro na jihar da ma wadanda ba na jihar ba domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ya kara da cewar rundunar ta shirya ganin ci gaban Kungiyar hadin kan al’umma da ‘Yansanda da Babban Sufeton ‘Yansanda Alhaji Usman Alkali Baba ya assasa domin inganta gudunmuwar da al’umma ke badawa ga magance ayyukan batagari.
Kwamishinan ya jaddada cewar babu wani hurumi ga jami’in dansanda da zai karbi wayar tafi da gidanka daga Jama’a domin gudanar da bincike, sai dai idan ana zargin ana yin amfani da ita wajen aikata laifi kuma binciken sai a Ofishin ‘Yansanda.