Kungiyoyin Al’umma sun bukaci da a bunkasa noman rani.

Kungiyoyin Al’umma sun bukaci da a bunkasa noman rani.

Kungiyoyin Al’umma a jihar Kwara sun yi kiran da a canza tafiyar bunkasa noman damina zuwa na rani domin samar da abinci.
Kungiyoyin sun yi kiran ne a wata sanarwar bayan taron musayar ra’ayi da suka gudanar ranar Alhamis a garin Ilorin a kan Kasafin Kudin jihar Kwara na 2023 a kan harkar noma.
Sun bayyana cewar harkar noma da kuma canjin yanayi shigar gizagizai suke yi wa juna, don haka kamata ya yi a jajirce wajen canza raja’a da ake yi ga noman damina zuwa noman rani.
Sun nuna bukatar kari a cikin Kasafin Kundin da aka yi wa bangaren noma daga kashi 3.59 zuwa kashi 10 cikin 100 ta yadda zai tafi daidai da kudurorin Maputo da Malabo.
Taron ya kuma bukaci da a mayar da hankali a kan kula da kasafin da aka yi wa harkar noma maimakon surutu a kan alkaluman.
Kungiyoyin sun kuma yi kira ga Ma’aikatar noma da Bunkasa Karkara ta fuskar Kungiyoyin Al’umma da Kungiyar Kananan Manoma Mata ta Nijeriya wajen shirya Kasafin Kudin domin ci gaba da yadda aka faro a 2020.
Sun bukaci da a kafa wurin ajiye amfanin gona domin rage asarar da ake yi bayan an kammala girbi.
Daga nan sai suka bukaci gwamnati da ta daga darajar rumbunan gargajiya domin bada kwarin gwuiwar ajiyar amfanin gona ta yadda za a rage lalacewa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya bada rahoton cewar Kungiyoyin sun hada da Cibiyar tallafawa al’umma da kawar da fatara da sauransu da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *