Shugaba Muhammadu Buhari zai karrama Sanata Bamidele da lambar girmamawa ta kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari zai karrama Sanata Bamidele da lambar girmamawa ta kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da karrama Sanata mai wakiltar Ekiti Opeyemi Bamidele da lambar girmamawa ta kasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya sami kofen takardar karramawar a ranar Alhamis a Abuja inda ta nuna cewar za a gudanar da bikin karramawar a ranar 11 ga watan Okutoba a Abuja.
Ofishin yada Labarai na Sanatan ya fito da wata sanarwa cewar sunan Sanata Bamidele wanda shine Shugaban Kwamitin Harkokin Shari’a da ‘Yancin Bil-Adama na cikin jerin sunayen wadanda za a karrama da lambar girmamawa ta kasa ta CON a 2022.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewar Sanata Bamidele shine kuma Shugaban Kungiyar ‘Yan Majalisar Dattawa na Kudancin kasar nan.
Ministan Ayyukan Musamman da Harkokin Huldar Gwamnati da Gwamnati Sanata George Akume ne ya sanya hannu a takarar karramawar a ranar 16 ga watan Satumba.
Bikin karramawar kamar yadda sanarwar ta nuna, za a gudanar da shine Babban Dakin Taro na kasa da kasa a Abuja ranar Talatar 11 ga watan Okutoba da misalin karfe 9:00 na safe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *