‘Yan Bindiga Sun Koma Amsar kwanon Shinkafa A Matsayin Fansa A Kaduna

‘Yan Bindiga Sun Koma Amsar kwanon Shinkafa A Matsayin Fansa A Kaduna

A Wani labari da Jaridar Leadership ta wallafa Wasu ‘yan bindiga da suka addabi yankin karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna sun kashe wani mazaunin garin tare da yin garkuwa da mutane 20.

Sai dai sun sako wasu mutane shida da suka yi garkuwa da su a ranar Asabar din da ta gabata bayan da suka karbi shinkafa ‘mudu’ guda 20, ‘mudu’ wake 20, mai lita 25, man gyada 25, da katunan waya na N10,000 a matsayin kudin fansa.

A wani labarin kuma, an rahoto cewa ‘yan bindigar sun kashe wani manomi a ranar Talata tare da yin garkuwa da wasu 20 a gonaki daban-daban a yankin Jangali da Kwaga na Birnin-Gwari a ranar Laraba.

Ƙungiyar Birnin-Gwari Emirate Progressive Union (BEPU) a takaice, sun bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya ta hannun shugaban kungiyar, Ishaq Usman Kasai.

BEPU ta kuma ce ‘yan bindigar sun kuma sanar da wasu al’ummomi da suka hada da Kwaga, Kwanan-Shehu, Unguwan Liman da Unguwan Shekarau da su biya harajin da ya kai Naira miliyan 12 kafin a bar su su girbe amfanin gonakinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *