Kashi 80 na hadurra na afkuwa ne sanadiyyar kuskuren Bil-Adama.
Kwamandan Shiyya na Rundunar Kiyaye Hadurra ta Kasa mai kula da Babban Birnin Tarayya da jihar Neja Mista Shehu Mohammed ya bayyana cewar Kashif 80 cikin 100 na hadurran dake afkuwa a fadin jihohi 36 na kasar nan hadi da Abuja na afkuwa sanadiyyar kuskuren Bil-Adama.
Ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a ranar Talata a Abuja.
Ya bayyana cewar shaye-shayen miyagun kwayoyi da barasa da dundumi da kuma gudun wuce sa’a na daga cikin manyan matsalolin dake haddasa hadurra.
A cewarsa kuskuren Bil-Adama yana taimakawa ga kashi 80 cikin 100 na hadurran dake afkuwa domin Bil-Adama ne ke sarrafa ababen hawan.
Ya yi nunin cewar direba ne fa zai fara tuki daga Kano ya biyo ta Abuja ya kuma nufi Kudancin kasar nan ba tare da ya huta ba, wanda hakan yana gayyatar hadari ne da kanshi.
Mohammed yace rashin kula da abin hawa ma na daga cikin kuskuren Bil-Adama, don haka ya shawarci direba da mamallakin abin hawan da su rika kulawa da lafiyar motocinsu.