Yajin Aikin ASUU: Jami’ar Calabar ta yi rashin malamanta fiye da 21.

Yajin Aikin ASUU: Jami’ar Calabar ta yi rashin malamanta fiye da 21.

Fiye da malaman Jami’ar Calabar 21
da suka hada da masu matsayin Farfesa da manyan malamai ne suka rasa rayukansu a Jami’ar sanadiyyar yajin aikin da ASUU ke cikin gudanarwa a halin yanzu.
Rasa rayukan irin wadannan malaman na ta karuwa a kullum
a Jami’oi daban daban na kasar nan.
Idan za a iya tunawa, Kungiyar ASUU ta gudanar da yajin aikin gargadi na tsawon wata daya a ranar 14 ga watan Fabrairun bana a kan gazawar Gwamnatin Tarayya na magance bukatunsu da kuma na Jami’oi mallakar gwamnati, inda tun daga wannan lokaci kofofin Jami’oin suka kasance a rufe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *