Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Katsina Alhaji Ibrahim Bako ya bayyana shirin hukumar na gudanar da sahihin zaben kananan hukumomi da ake shirin gudanarwa a Satan Aprilun wannan shekara.
Ibrahim Bako ya bayyana hakan ne a Katsina lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishin sa dake hukumar zaben.
Kamar yadda ya bayyana shirye shirye sunyi nisa wajen tsare tsaren da hukumar keyi domin gudanar da zaben a dukkanin kananan hukumomin jihar, yana mai cewa kawo yanzu hukumar ta rigaya ta fara kafa sunayen masu zaben a dukkanin mazabun jihar domin wadanda suka cancanci Kada kuri’a su duba sunayen su cikin lokaci
Yace yin hakan na da nufin tabbatar da dukkanin wadanda suka cancanta sun shirya gudanar da zaben cikin lokaci domain tabbatar da shimfida adalci da zai ba kowa damar amincewa da shirin zaben
Ibrahim ya bayyana cewa tsarin da hukumar tayi Wanda ke dai dai da ka’idojin zaben ya baiwa kowace Jam’iyya damar aje wakilinta a kowace rumfa lokacin da zaben zai gudana da nufin yi ma kowace jam’iyya adalci ta lura da akwatinta
Kamar yadda ya bayyana a zaben kansiloli ma,da zaran an kammala jefa kuri’a za’a kidaya kuri’un a gaban kowane wakili tare da bayyana jam’iyyar da ta samu nasara nan take a mazabar ba tare da zuwa ko’ina ba
Shugaban hukumar zaben ta jihar Katsina ya bada tabbacin sa na hada hannu da hukumomin jami’an tsaro domin tabbatar da zaben kananan hukumomin ya gudana cikin zaman lafiya da lumana,tare da kira ga al’ummar jihar su bada goyon baya domin ganin hukumar ta samu nasarar gudanar da sahihin zaben da kowa zai amince da shi
Ya bayyana cewa hukumar na cigaba da wayar da kan jama’a mahimmancin zaben ta hanyar kwamitocin masu ruwa da tsaki da kuma ta kafafen watsa labarai domin samun nasara.