Jami’ar jihar Filato ta sabbin Na’iban Mataimakan Shugaban Jami’ar.
Jami’ar jihar Filato dake Bokkos ta nada Farfesa Pyefa Galadima da Dokta Jurji Gomos a matsayin Na’iban Mataimakan Shugaban Jami’ar a sashen koyo da koyarwa da kuma sashen mulki kamar yadda suke a tsare.
Jami’in hulda da Jama’a na Jami’ar Mista John Agam ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Talata a garin Jos.
Sanarwar ta bayyana cewar an sanar da nadin ne jim kadan da kammala taron Majalisar Koli ta Jami’ar da aka gudanar ranar Litinin.
Sanarwar ta kara da cewar nada manyan Jami’an biyu dake da tsawon wa’adi na shekaru biyu ya fara aiki nan take.
Jami’in hulda da Jama’ar ya bayyana cewar Majalisar Kolin Jami’ar ta amince da ranar 10 ga watan Okutoba ta zamo ranar komawa Jami’ar domin fara zangon karatu na 2020/2021 da kuma 2021/2022 ga sabbin dalibai.
Ya bayyana cewar sabbin dalibai zasu dawo Jam’iyyar domin kammala yin rajista da kuma shirin daukar lacca.
Mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Yohanna Izam ya taya sabbin Na’iban da aka nada sannan ya yi kira garesu da su ba marar da kunya wajen gudanar da aikinsu.