‘Yan Nijeriya 500,000 ne ke jiran a kwasosu daga kasashe uku.
Kwamishinar Tarayya a Hukumar kula da ‘yan gudun hijara da wadanda suka rasa mauhallinsu Imaan Suleiman Ibrahim ta bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Birnin New York a babban taron Majalisa Dinkin Duniya karo na 77 cewar za a kwaso ‘yan gudun hijara daga kasashen Nijer da Chadi da kuma Kamaru.
Ta bayyana cewar wadanda za a kwaso nan gaba sun hada mutane 1,000 kuma aikin kwasosu abin sha’awa ne dake faruwa, kuma ana kula dasu sosai idan sun dawo.
A cewarta, akwai Kwamitin Shugaban Kasa a kan kwaso’yan gudun hijarar a Shiyyar Arewa maso Gabashin kasar nan wanda zai tallafawa kokarin Tawagar gudanar da aikin kwaso ‘yan gudun hijarar wanda keekarkashin jagorancin Hukumar.
Ta bayyana cewar aikine wanda ake cikin gudanarwa kuma an fara aikin