Za a hanzarta tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Anambra.

Za a hanzarta tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Anambra.

Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya yi alkawarin hazarta daukar matakin tallafawa wadanda suka fuskanci iftila’in ambaliyar ruwa a jihar.
Gwamnan wanda Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin jihar Mista Ernest Ezeajughi ya wakilta a lokacin gudanar da rangadin yankunan da iftila’in ya shafa domin auna kalubalen dake fuskantar yankunan da kuma mizanin barnar da ambaliyar ruwan ta haddasa.
Shugaban Ma’aikatan, wanda ya sami rakiya Babban Sakataren hukumar samar da agajin gaugawa na jihar Sir Paul Odenigbo, yace Gwamnan ya umurci da a gudanar da rangadin sakamakon ankarar da shi da mazauna yankunan suka yi.
Shiko tsohon Shugaban Karamar hukumar Ogbaru Mista Arinze Awogu kira ya yi ga gwamnatin tarayya da ta jihar da su hanzarta ceto jihar domin tana gaf da nutsewa.
Ezeajughi ya bada tabbacin cewar gwamnatin jiha zata hada hannu da gwamnatin tarayya domin tabbatar da ganin an gudanar da aikin kwashe al’umma tare da dukiyoyinsu.
A cewarsa duk wani abu da ya kamata a yi za a yi cikin hanzari domin rage matsalolin da wadanda abin ya shafa tare da tsare rayuka da dukiyoyinsu.
Da yake jawabi a wajen, dan takarar Majalisar Tarayya na Mazabar Tarayya ta Ogbaru a Jam’iyyar APGA Mista Awogu ya yabawa Gwamna Chukwuma Soludo a kan nuna damuwa ga jin dadin al’ummar yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *